Coronavirus: Gwamna Ikpeazu na  Abia  ya mika wa mataimakin sa ragamar mulkin sakamakon kamuwa da cutar

Gwamnan  jahar Abia, Okezie Ikpeazu, ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishinan labarai na jahar,John Okiyi Kalu, ne ya fitar da sanarwar a ranar litinin, wanda ke nuna cewa, tuni  dai aka killace Gwamna Ikpeazu.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya umarci mataimakinsa ya jagoranci jahar a matsayin riko zuwa ranar da gwamnan ya samu lafiya.

A ranar Asabar, 30 ga watan Mayu 2020 ne, Gwana Okezie Ikpeazu don radin kansa ya amince a yi masa gwajin COVID-19 kuma ya bayar da umarni a yi wa ‘yan majalisar zartarwar jahar gwajin.

Sakamakon gwajin ya nuna cewa Gwamna Ikpeazu ba ya dauke da cutar, a ranar Talata 2 ga watan Yuli 2020, cewar Kwamishinan.

Sai dai a ranar Alhamis 4 ga watan Yuni 2020, gwamnan ya sake mika samfur ga hukumar  dakile yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC, inda gwaji ya nuna cewa yana dauke da  kyawar cutar ta Covid19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More