Coronavirus: Gwamnatin jahar Zamfara ta fara rabon kwai

Jahohin da ba’a samu bullar Coronavirus  ba a kasar Najeriya sun shiga daukar matakan ko-ta-kwana ganin yadda cutar ta kai zuwa jahohin da ke makwabtaka da su.

Jahar Zamfara tana daga cikin jahohin da cutar ba ta bulla ba, amma hukumomi a jahar sun ce suna daukar matakan kariya tun yanzu, saboda mai kwarmin ido da wuri ya ke soma kuka.

Kakakin majalisar dokokin jahar Nasiru Mu’azu Magarya, wanda  shi ne  kuma shugaban kwamitin ko-ta-kwana kan yaki da Coronavirus  ya shaida wa BBC cewa, ganin yadda cutar ta bulla a jahohin da suke da makwabtaka da su shi ya sa suka tashi tsaye don shirin ko-ta-kwana.

Inda  daga cikin matakan da suka dauka sun hada da bawa jami’an kiwon lafiya horo na musamman, sannan an tanadi wuraren uku da za a ajiye wadanda suka kamu da cutar idan har ta bulla a jahar,kayayyakin kariya daga kamuwa da cutar kamar su takunkumin fuska, abin wanke hannu da dai makamantansu inji kakakin majalisar dokokin jahar.

 Sakamakon dokokin da aka sanya na hana fita da walwala ga al’ummar jahar, gwamnati ta tanadi abubuwan da za a rabawa mutane don a rage musu radadin zaman gida.

Tuni aka fara raba abubuwan da suke saurin lalacewa daga cikin kayayyakin abinci kamar irin kwai wanda aka raba shi a dukkan kananan hukumomin jahar goma sha hudu, wanda kwan na daga cikin irin gudunmuwar da suka fara samu, kuma bada jimawa ba za a fara raba kayan abinci kamar su gero, dawa, shinkafa da dai sauran kayan abinci. Inji Nasiru Magarya

Zuwa yanzu dai ba a samu bullar cutar korona a jahar Zamfara ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More