Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta bawa WHO hadin kai don gwajin maganin cutar a jahohi guda shida

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amincewa wa Hukumar Lafiya ta Duniya wata WHO gwada maganin cutar ta Covid19  a jahohi guda shida na Najeriya.

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana cewa, za a gwada maganin a  jahohin Legas, Kaduna, Sokoto, Kano, Ogun da kuma birnin tarayyar Abuja.

Ministan ya bayyana hakkan ne a ranar Litinin a wajen taron kwamitin yaki da cutar Covid19  na shugaban kasa.

Magagunna da za’a sanya idanu a kan su kafin a gwada a kan mai cutar, sun hada da Remdesivir,Chloroquine ko hydroxychloroquine, Lopinavir, da kuma  Ritonavir.

Gwajin ingancin maganin  na duniya yana  daga cikin kokarin hukumar lafiyan na samar da magani da kuma riga-kafin Coronavirus a cikin kankanin lokaci.

Jahohin Kogi da Cross River zuwa yanzu  ba a samu bullar Coronavirus ba, amma kwararru daga ma’aikatar lafiya tare da hukumar NCDC za su garzaya birnin Calabar don bada  tallafisu kan harkokin na lafiya. Inji minista Ehanire

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More