Coronavirus: Jahohin Arewa sun fara bude masallatai da coci-coci

Wasu daga cikin jahohin arewacin Najeriya za su bude wuraren ibada da aka rufe na tsawon makonni bisa yunkurin daƙile yaɗuwar Coronavirus a kasar.

Jahohin sune:
Borno, Adamawa, Gombe da Jigawa

Kuma sun sassauta dokar wadda ta haramta yin taruka ciki har da na addini kuma yanzu mazauna yankunan za su iya zuwa masallatan Juma’a da majami’u.

Kazalika an bude babbar Kasuwar Dabbobi ta Adamawa bisa sharadin za a bi ka’idojin bada tazara tsakinin ka da wani na taku shida.

A bagaren Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa ya bayyana cewa, sun bada sharuda kan cewa duk wadanda zai shiga masallaci sai ya wanke hannayensa sannan ya saka takunkumi da kuma bayar da tazarar mita biyu [tsakanin sahun salla]. Yawanci ana yi wa masallatan feshi kafin sallar Juma’a.

Jahohin sun ce zuwa yanzu al’amura sun fara daidaituwar da za ta sa a sassauta tare da bude wuraren ibadar, kuma abin da ya sa suka yi hakan kenan.

BBC ta rawaito cewa, kazalika wasu malaman addinin Musulunci sun yi kira ga gwamnatin jahar Kano ta sake bude masallatan Juma’a domin su yi salloli kamar yadda aka saba a baya.

Wasu daga cikin limaman masallatan sun bayyana fatansu na ganin matakin ya taimaka wurin dakile cutar ta Covid19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More