
Coronavirus: Jumullar mutane da cutar ta kashe a kasar Najeriya sun doshi 1000
An samun karin sabbin mutane 290 da suka kamu da cutar ta Covid19 a kasar Najeriya, wanda hakkan ne ya bada jumullar 46,867 da ke dauke da kwayar cutar.
Sabbin wayanda suka kamun sune:
Lagos-82
Plateau-82
Oyo-19
FCT-18
Edo-16
Kaduna-15
Enugu-9
Ogun-9
Kano-8
Kwara-8
Cross River-5
Ondo-5
Rivers-5
Ekiti-4
Imo-3
Borno-2
An sallami mutane 33,346 da suka warke daga cutar, inda hukumar NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 950 daga ranar Litinin 10 ga watan Agusta 2020.