Coronavirus: Kalubalin da NCDC ke fuskanta a Najeriya

Hukumar takaita yaduwar cututtuka ta Najeriya wato  NCDC ta ce tana fuskantar manyan kalubale a fagen yaki da cutar covid-19 wadda ta zamto annoba a sassan Duniya.

Shugaban hukumar dakta Chikwe Ihekweazu, shi ne ya bayyana hakan da cewar yaga kwazo da nagartar ma’aikatar lafiyar kasar Najeriya  wajen lalubo wadanda ake zargi sun harbuwa da Coronavirus.

Legit ta rawaito cewa, dakta Ihekweazu  ya bayar da shaidar yadda hukumar ke fuskantar kalubale wajen aiwatar da gwaji kan wadanda ake zargi domin tabbatar da sun harbu da cutar ko kuma sabanin haka, wanda a yanzu Najeriya tana da ikon aiwatar da gwajin kan mutane 1,500 a kowace rana.

Dakta Ihekweazu ya bayyana hakkan ne  yayin ganawa da kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa kan dakile  cutar Covid-19 a Najeriya.  A jawabin da Shugaban  kasar Najeriya Muhammadu Buhari  ya gabatar na ranar Litinin, ya bukaci hukumar NCDC ta kara himma wajen aiwatar da gwajin mutum 2000 a kowace rana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More