Coronavirus: Kasar  Saudiyya ta hana shiga Makkah da Madina

Saudiyya ta fitar da  sanarwar hana maniyatta aikin Hajji da Umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi.

Ma’aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana ‘yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma zuwa kasar mai tsaki.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta wallafa a shafin Twitter ta kuma ce ta dakatar da amfani da katin shaidar dan kasa maimakon fasfo lokacin shiga da fita daga Saudiyya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More