Coronavirus: Kashi 60 na bashin da ake bin tashoshin watsa shirye-shirye   gwamnatin Najeriya  ta yafe masu

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, tayi   wa gidajen rediyo da talabijin rangwamin kashi 60 cikin 100 na basukan da ta ke binsu.

Gwamnatin ta bayyana  cewar, tana bin wasu kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin bashin kudade da ya kai naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas.

Cikin wata sanarwa, ministan yada labarai na  kasar, Lai Muhammad, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don rage musu radadin rashin kudaden shiga saboda annobar cutar Coronavirus .

Duk wadanda ake bi bashin su hanzarta biyan kashi arba’in cikin dari na abin da ake binsu cikin watanni uku. Cewar Lai Muhammad

Sanarwar ta kara da cewa gidajen rediyo da dama a Najeriya ana binsu bashi mai yawa lamarin da ya sa wasu ma ke fuskantar barazanar kin sabunta musu lasisin su.

Shugabar Kungiyar kafafen watsa labarai na rediyo da talbijin a Najeriya kuma shugabar gidan talbijin na Abubakar Rimi a Kano, Hajiya Sa’a Ibrahim,  ta ce sun yi farin ciki da wannan matakin.

“Ko ya ya idan aka yi maka abu, dole za  ka ji dadi kuma ka yaba,  abin da yake akwai shi ne an yi abin da za a ce ai da babu gwara ba dadi.”

“Wannan ma tun da ya wuce rabi za a ce an yi hobbasa to amma dai abin da yake akwai shi ne dole za a bibiya kowa ya ma san matsayin bashin da yake kansa, kafin mu tafi  ga biyan ,” in ji Hajiya Sa’a

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More