Coronavirus: Kwamitin yaki da cutar ta bai wa Buhari shawarar bude masallatai da makarantu

Kwamitin gwamnatin tarayyar Najeriya da ke yaki da Coronavirus ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarar sake bude wuraren ibada, makarantu da kuma kasuwanni.

Kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 ya mika wani bangare na shawarwari kan sake kwarya-kwaryar bude karin harkokin kasuwanci, makarantu da wuraren ibada domin Shugaba Buhari ya yi nazari, a cewar Sakataren Gwamnatin Tarayyar Boss Mustapha, to bayan ganawa da shugaban kasa.
Mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmed , ya fitar da sanarwar hakkan ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 1 ga watan Yuli 2020.

Da ma dai tuni wasu jahohin na kasar ta Najeriya suka bari a bude wuraren ibada, Amma dai sun ce dole mutane su dauki matakan kariya, Dan kare kansu, dama kuma gudun yaduwar cutar ta Covid19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More