Coronavirus: Mataimakin gwamnan jahar Bauchi Baba Tela ya kamu da cutar

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa mataimakinsa Sanata Baba Tela ya kamu da Coronavirus.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, Gwamna Bala ya ce Baba Tela ya kamu da cutar ta Covid19 ne a bakin aiki, kasancewar sa shugaban kwamitin yaki da cutar na jahar ta Bauchi

Tuni dai aka killace mataimakin nasa, Tela, yayin da ma’aikatan lafiya kuma suke bashi kulawa da ya kamata. Inji shi.

Gwamna Bala ya kara da ce an gudanar da gwajin cutar ta Covid19 a kan mutanen da ya yi mu’amala da su, sannan an shawarce su, da su killace kansu har sai an fitar da sakamakon gwajin.

Gwamnan ya jajantawa mataimakin nasa, iyalansa tare da yi masa addu’ar samun sauki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More