Coronavirus: Mutane 27 ne suka kamu a Kano

Adadin mutanen  27 ne  suka kamu da Coronavirus a jahar Kano zuwa yanzu.

Ma’aikatar lafiyar jahar Kano  ce ta tabbatar da karin mutane 6 da suka kuma da kwayar  cutar a ranar  Juma’a 17 ga watan Aprilu, da misalin   karfe 10:56 na dare, a shafin ta na Twitter.

 Yanzu dai Kano ita ce ta uku wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya,inda ma cutar tayi sanadin mutuwar mutum daya a ranar Laraba.

An samu bullar Covid19 a jahar Kano ranar 11 ga watan Aprilu 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More