Coronavirus: Mutanen da suka warke a Duniya sun haura miliyan daya

Adadin wadanda suka warke daga annobar Coronavirus a fadin Duniya sun zarta miliyan daya, a cewar sabbin alkaluman Jami’ar Johns Hopkins da ke Amurka.

Mutum 1,014,931 ne jami’ar ta ce sun warke, kuma Amurka ce kan gaba a yawan wadanda suka warke din da kuma wadanda suka kamu da cutar.

Amurka: 153,947 (cikin jumillar mutum 1,070,026)

Jamus: 123,500 (cikin jumillar mutum 163,009)

Spaniya: 112,050 (cikin jumillar mutum 213,435)

China 78,523 (cikin jumillar mutum 83,956)

Italiya 75,945 (cikin jumillar mutum 205,463)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More