Coronavirus: NNPC ta bada kyautar asibiti a Abuja

Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari ya bayar da gudummar asibiti ga hukumomin birnin tarayyar Abuja mai cin gado 70 a madadin kamfanin, don bada kulawa ga masu annobar coronavirus.

Ministan Abuja Malam Mohammed Musa Bello wanda ya jagoranci tawagar hukumar birnin (FCTA) zuwa wurin taron, ya gode wa kamfanin NNPC bisa ayyukan ci gaba da ya saba kawo wa birnin, da kuma daukacin ma’aikatar mai da iskar gas dangane da tallafin da suke bai wa Abuja, kan a yaƙi da annobar Coronavirus da kuma rawar da NNPC ke takawa a ci gaban birnin Abuja na tsawon shekaru.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More