Coronavirus: Shugaba Buhari ba zai jawabi ga yan’ Najeriya ba- Femi Adesina

Mai magana da yawun shugaba Buhari, kan harkokin labarai wato Femi Adesina ya fitar da sanarwar  cewa, Shugaba Buhari ba zai yi jawabi wa Yan’ Najeriya  ba dangane matakin da kasar za ta dauka a gaba, illa dai gwamnoni su yi aiki tare da Kwamitin Shugaban Kasa na  yaki da annobar Coronavirus (PTF)

Mista Femi ya ce Shugaba Buhari ya riga ya tattauna da gwamnoni dangane da al’amarin ta kafar intanet a ranar Litinin kuma “ya umarci gwamnoni da su bawa kwamitin hadin kai”. Shugaba Buhari ne zai yanke hukuncin kan cigaban sassaucin dokar  ta hana fita ko kuma zabanin hakkan, cewar mista Femi.

Dama dai babban jami’i a kwamitin yaki da Coronavirus ta fadar shugaban kasa, Dr Sani Aliyu na ya bayyana ranar Lahadi cewa kwamitinsu ya mika wa Buhari shawarwarinsa kuma zai sanar da matakin da za a dauka ranar Litinin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More