
Coronavirus: Shugaba Buhari ya bada umarnin karbo maganin cutar na gargajiya
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin karbo kason Najeriya na ganyen shayin Madagascar da shugaban kasar ya ce yana maganin cutar ta Covid19
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da Coronavirus ne ya bayyana haka a jiya Litinin 11 ga watan Aprilu yayin da yake ganawa da manema labarai kan cutar Coronavirus a kasar Najeriya da kuma matakan da gwamnati ke dauka. Ya bayyana cewar,duk da cewa shugaba Buhari ya amince a karbo maganin na Madagascar, sai ya bi tsari na tabbatar da ingancin magunguna.
Madagascar tuni ta aika wa kasashe da dama na Afirka da maganin kyauta, kuma ta tura zuwa Guinea Bissau,inda
Najeriya ta ce ya kamata ta karbo nata kason daga Guinea Bissau. Zuwa daren Litinin dai , hukumar NCDC ta tabbatar da mutune 4,641 wayanda suka kamu da cutar ta Covid19 a Najeriya, inda mutune 902 suka warke yayin da mutum 150 suka riga mu gidan gaskiya.