Coronavirus: Shugaba Buhari ya bukaci a kula, karfafa gwiwa batare da anji tsoro ba

Fadar shugaban Najeriya ta ce ganin arha ne da zuzuta abu, suka sa wasu mutane ciki har da ‘yan majalisar kasar, suke yekuwar neman suna a wajen talakawa kan batun covid-19.

Ta ce wannan, ba lokaci ne na neman shiga a wajen talakawa da siyasar ganin arha ba.

Sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar da yammacin jiya na cewa jazaman ne sai duk ‘yan kasar Gabas da Yamma, Kudu da Arewa su hada kai a yaki da wannan annoba, ba tare da la’akari da bambancin addini ko akida ba.

Fadar shugaban Najeriya ta ce ba ta son tayar da hankula, amma dai za su ci gaba da fitar da sabbin bayanai masu fa’ida ga ‘yan kasar,cikin matakan da hukumomi ke dauka don yaki da cutar coronavirus har da sanarwar da Babban Bankin Najeriya ya fitar a ranar Litinin ta samar da rancen naira tirliyan 1 da biliyan 100 ga harkokin kasuwancin da wannan annoba ta shafa.

Haka zalika, bankin ya samar da wani asusun ba da tallafi ga magidanta da masu kanana da matsakaitan sana’o’i da kuma sanar da rage kudin ruwa a kan basuka daga kashi 9% zuwa kashi 5%

Haka shi ma, Kamfanin samar da man fetur na kasar NNPC ya sanar da ragin naira 20 a kan litar man fetur guda, daga naira 145 zuwa naira 125 a yanzu.

“Annobar covid-19 ta janyo faduwar farashin danyen man fetur a duniya, don haka shugaban kasa ya ce su ma ‘yan Najeriya, ya kamata su ci moriyar wannan ragi da aka samu” in ji sanarwa.

BBC ta rawaito cewa, fadar shugaban ta ce suna da babban kwamitin hadin gwiwa na shugaban kasa karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Kuma a cewarta an bai wa kwamitin damar gudanar da duk wasu nauye-nauye kan wannan lamari.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce: “Muna kuma yin kira ga ‘yan Najeriya kada su dubi wannan hali da aka shiga a matsayin wata damar nuna siyasa ko amayar da kullatar da suke da shi ga gwamnati ko kuma jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa duk jami’an da ke kan gaba-gaba a yakin da Najeriya ke yi da mummunar cutar coronavirus wacce aka sauya maya suna da Covid 19 da ta addabi duniya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More