Coronavirus ta bulla a jahar Kogi inda cutar ta kashe mutane 254 a kasar Najeriya

Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya  ta fitar a daren Laraba sun nuna cewa an samu mutane 389 wadanda  suka sake  kamuwa  da Coronavirus, wanda hakkan ne yasa adadin masu cutar a Najeriya suka kai 8,733.

Sabbin wayanda suka kamun sune:
Lagos-256
Katsina-23
Edo-22
Rivers-14
Kano-13
Adamawa-11
Akwa Ibom-11
Kaduna-7
Kwara-6
Nasarawa-6
Gombe-2
Plateau-2
Abia-2
Delta-2
Benue-2
Niger-2
Kogi-2
Oyo-2
Imo-1
Borno-1
Ogun-1
Anambra-1

Sannan hukumar ta NCDC ta tabbatar, da cewa,  mutane 2,501 suka warke daga cutar, inda mutane 254 suka rigamu gidan gaskiya  A karon farko Coronavirus  ta bulla jahar Kogi inda aka samu mutum biyu sun kamu da cutar.

Dama dai a dukkan jahohin Najeriyar, jahohi biyu ne kawai suka rage wanda cutar bata bulla ba, wato  jahar Kogi da kuma Cross River, amma a daren ranar  Laraba 27 ga watan Mayun ne alkaluman da  NCDC ta fitar na wadanda suka sake kamuwa ya nuna har da jahar ta Kogi.

Sai dai kuma a babban birnin tarayyar Abuja an shafe kwanaki biyu ba a samu wadanda suka kamu da cutar ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More