Coronavirus ta bulla a jahar Plateau

Gwamnatin jahar Plateau ta fitar da sanarwar cewa, a karon farko an samu mai cutar Covid 19 a jahar.

Hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC ce ta tabbatar da hakkan a ranar Alhamis.

Sanarwar wadda aka fitar a shafin Twitter, ta nemi ‘yan jahar da su kwantar da hankalinsu kasancewar suna daukar matakan da su ka dace,wajen hana yaduwar cutar.

Dokar kulle da gwamnatin ta saka ya kawo karshe a ranar Juma’a.

Sai dai kuma gwamna Lalong ya ce za a dan sarara har zuwa ranar Litinin 27 ga watan Afrilu, sannan dokar kullen ta cigaba da aiki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More