Coronavirus ta sanya likitoci sun fara yajin aiki a Abuja

Kungiyar likitocin Najeriya reshen Abuja babban birnin kasar ta soma yajin aiki duk da yake an samu bullar cutar Corbid-19 a kasar.

Sanarwar da shugaban kungiyar likitocin, Roland Aigbovo, ta ce dukkan likitocin da ke aiki a gudunma 14 na Abuja da manyan asibitoci da cibiyoyin lafiya sun soma yajin aiki ranar 16 ga watan Maris domin tursasa wa gwamnatin birnin ta biya su albashi.

“Mambobinmu sun fada matsanancin halin rashin kudi saboda rashin biyan su albashi kamar yadda ya kamata kuma mun jira har karshen 2019 da kuma sabuwar shekarar 2020, har zuwa makonni uku na watan Fabrairu domin a biya mu albashin watan Janairu wanda bai taka kara ya karya ba,” in ji sanarwar.


BBC ta rawaito cewa mista Aigbovo ya ce matakin da suka dauka na da wahala amma babu yadda za su yi idan basu dauke shi ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More