Coronavirus: Yadda aka yi gwamna Akeredolu gano ya kamu da cutar

Gwamnan Jahar Ondo, Rotimi Akeredolu Ya Kamu Da Cutar Coronavirus

Gwamnan  Ya bayyana hakan ne a kan shafinsa na Twitter a ranar Talata 30 ga watan Yuli 2020,  inda ya ce an yi masa gwajin cutar ne bayan da ya gama jinyar cutar Malaria.

Gwamnan ya  kuma bayyana cewa wani gwamna ne ya ba shi shawarar zuwa a yi masa gwajin cutar, a wajen taron majalisar zartarwa na jam’iyyar APC a da ka gudanar birnin  Abuja.

Inda yace gwajin da aka masa  ya nuna cewa yana dauke da Covid19.

“Babu Alamomin  cutar a tare dani ba, kuma har na kilace kaina, zan cigaba da aiki. Ina mutukar godiya da a taya ni addu’o’i don samun sauki”. Inji gwamna Rotimi Akeredolu .

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More