Coronavirus: Yadda ake ciki a jahar Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa, zuwa safiyar yau Litinin 1 ga watan Yuni 2020, cutar ta Covid19 ta kama mutune 256 a jahar.

Gwamnatin ta ce an sallame mutane 157 dasu ka warke daga cutar, wanda zuwa yanzu mutune 93 ne ke fama da kwayar cutar.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter

A cewarta, an yi wa mutune 1649 gwajin cutar jumulla, yayin da mutum 8 suka rigamu gidan gaskiya. Sannan kuma gwamnatin ta bukaci mutane su ci gaba da zama a gida suna daukar matakan kare kansu daga cutar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More