Coronavirus: Yanzu mutane 12 ne suka kamu a Najeriya

An samu sabbin mutane 4 da suka  kamu da coronavirus a jahar Lagos inji kwamishinan lafiya na jahar.

Hakkan yasa masu cutar suka karu zuwa guda 12 a Najeriya.

Kwamishinan lafiya na Legas Akin Abayomi ya bayyana wa ‘yan jarida samun sabbin mutanen da ke dauke da cutar ne a sakatariyar jahar ranar a yau Alhamis19 ga watan Maris 2020, inda yace an yiwa mutane 19 da ake zargi kwaji,sannan aka sannar da mutane 5 da suka kamu a ranar Laraba.

Daga cikin mutanen akwai wadda ta koma Najeriya daga Faransa, da wani da bai yi tafiya ko ina ba amma aka gano yana dauke da cutar.

Sai kuma wani dan Najeriya da ya koma kasar daga Jamus ranar 13 ga watan Maris.

Kwamishinan ya ce a yanzu ana bin sawun mutum 1,300 da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar coronavirus wacce aka sauya mata suna zuwa Covid-19.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More