Coronavirus: Ya’ta ta killace kanta a gida dawowar daga Birtaniya-Aisha Buhari

Uwargidan Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta sanar da cewa ‘yarta ta killace kanta bayan dawowar Najeriya daga kasar Birtaniya, inda coronavirus ta fara yawa a can.

Aisha Buhari bayyana hakkan ne a shafin ta na Instagram a yau Alhamis 19 ga watan Maris 2020, sai dai bata bayyana sunan  ‘yar tata ba.

Ta ce yarinyar ta killace kan nata ne saboda shawarar da Ministan Lafiya na kasar suka bayar ba wai don ta nuna alamun cutar ba. Inda ta yi kira ga iyaye su dauki irin wannan matakin idan yaransu sun dawo daga tafiya.

Sannan kuma uwargidan shugaban kasar ta ce ta rufe ofishinta na tsawon mako biyu saboda wasu ma’aikatan ofishin nata sun dawo daga Birtaniya.

A karshe kuma Aisha Buhari ta yaba wa gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya bakwai da na jahar Neja da Kwara kan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar tare da yin kira ga mutane da su ci gaba da bin shawarwarin jami’an lafiya don kauce wa yaduwar cutar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More