Coronavirus: Za a fara rabun takumkumi guda miliyan daya a Kano

Gwamnan jahar Kano dakta Abudullahi Umar Ganduje ya ce zai raba wa al’ummar jahar takunkumi har guda milyan daya, a wani yunkurinsa na dakile cutar Covid19 a jahar ta Kano. Al’ummar jahar Kano sun samun zarafin yin zirga-zirga da zuwa kasuwanni dan yin cefane.

Gwamnatin ta bayyana cewa, ta kafa dokar tilasta wa mutanen jahar sanya takunkumin wato face mask a wuraren da jama’a suka taru wato cunkoso.

Gwamman jahar Abdullahi Umar Ganduje ne dai ya sanar da haka a yayin wata ganawa da ‘yan jarida a jiya lahadi, bayan lura da cewa jama’ar sun yin biris da wannan umarnin. Tuni dai muka tanadi kotunan tafi-da-gidanka inda da zarar an kama masu karya dokar za a hukunta su nan take. Inji gwamnan

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More