Coronavirus:Abunda sabuwar dokar da gwamnatin Najeriya ta sake dauka don kau da yaduwar cutar ta kunsa

Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban kasa da ke yaki da annobar Covid19 a Najeriya ya sanar sun hada da dage haramcin tafiye-tafiye tsakanin jahohi amma a lokutan da dokar takaita zirga-zirga ba ta aiki.

A cewar kwamitin dole ne duka tasoshin mota zu zama suna da na’urar auna zafin jiki da kuma tabbatar da ko wanne fasinja sai ya sanya takunkumi kafin ya shiga mota. Za kuma a fitar da wasu dokokin da ake bukatar duka tashoshin kasar su kasance suna bi.

Sauran matakan sun da hada da:

Za a fara zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida nan gaba amma kwamitin bai bayyana lokacin hakan ba. *Bude makarantu ga daliban da za su rubuta jarrabawar karshe wadanda suka hadar da ‘yan SS3 da JS3 da kuma Firamari 6 *Gidajen cin abinci za su ci gaba da kasancewa a kulle sai dai wadanda suke yi wa otel-otel girki *Mutane 20 ne kawai aka yarda su halarci jana’iza ko kuma daurin aure *Dakunan haska fina-finai da wuraren motsa jiki suma za su ci gaba da kasancewa a rufe *Ma’aikatan gwamnati za su ci gaba da aiki daga karfe 9 zuwa 2 na rana kamar yadda suke yi a yanzu *Samar da abin wanke hannu da sabulu a wuraren taron jama’a. *Tilasta amfani da takunkumi a taron jama’a

Kwamitin ya ce dokar kasuwanni za ta kasance kamar yadda ta ke a yanzu a fadin kasar.

A baya dai kwamitin ya ce an sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safiya, kuma dokar za ta ci gaba da kasancewa a haka.

Kwamitin shugaban kasa kan yaki da Coronavirus a Najeriya ya sanar da matakin rufe kananan hukumomi 18 cikin 774 da ke Najeriya.

A cewar kwamitin, wadannan kananan hukumomin su ne suke da kashi 60 cikin 100 na mutum 24,077 da suka harbu da cutar korona.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More