Coronavirus:An samu karin mutane 5 a Najeriya

An samu karin mutane 5 masu coronavirus a Najeriya in ji hukumar da ke kare yaduwar cututtuka ta kasar.
 
Hukumar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ce ta tabbatar da hakan a ranar Laraba 18 ga watan Maris 2020 a shafinta na Twitter.
 
Hukumar ta ce duka masu dauke da cutar sun dawo ne daga Burtaniya ko Amurka kwanan nan.
 
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an kiwon lafiya ke daukar dukkan matakan da ya kamata don yakar yaduwar cutar a kasar.
 
zuwa wannan lokacin dai an tabbatar da mutane takwas masu dauke da cutar a kasar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More