Coronavirus:Gida-gida za a fara bi a jahar Legos

Gwamnatin jahar Legos za ta fara bin gida- gida a yunkurin ta na dakile cutar ta Covid 19.

Kwamishinan lafiya na Legos, Najeriya ya gargadi mazauna birnin su shirya domin karbar bakuncin ma’aikatan lafiya wadanda za su rika bin su gida-gida don yin tambayoyi kan alamomin coronavirus.

Ma’aikatan lafiyar za su gudanar da tambayoyi kan alamomin  kamar haka:
Tari
Mura
Zazzabi

Za’a gudanar da hakkane dan gano wande ke dauke da cutar, in ji Farfesa Akin Abayomi a sakon Twitter da gwamnatin Lagos ta wallafa a shafin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More