Coronavirus:Gwamna El-rufa’i ya nemi yafiyar al’ummar jahar Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasir el’Rufai ya nemi yafiyar alummar jahar kan matakan dokar hana fita da ya sanya a yunkurin sa na dakile yaduwar annobar ta Covid19.

A matsayina na gwamnanku, ina neman yafiyar ku, amma matakin dokar na hana fita ya zama wajibi sai an ɗauka don gudun yaduwar cutar annoba, inji gwamna El-Rufa’i.

A Wani bidiyo da gwamna El-Rufa’i ya wallafa a shafinsa na Instagram, wanda yake zaune shi da matarsa, Aisha Garba El-Rufa’i a kan kujera suna gode wa al’ummar Kaduna da suka bi umarnin zama a gidajensu.

Gwamnan ya kara da cewa a matsayinsa na ganau ba jiyau ba, cutar Coronavirus tana da mutukar hadarin gaske kuma tana iya salwantar da rayuwar dan adam,sannan kuma hanya guda daya da zai kawo karshen cutar, shine hana mutane zirga-zirga.

A bangaren uwar gida tasa kuwa, Aisha,godiya tayi wa ma’aikatan lafiya kasancewarsu a kan gaba wurin yaki da cutar, tare da hukumomi masu zaman kansu duba da irin gudunmawar da suka baryar a wannan lokacin na rintsi, sannan ta jaddada kira ga al’umma da su ci gaba da zama a gida tare da bin hanyoyin da ya dace don kare kai daga cutar ta Covid19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More