Coronovirus: Najeriya ta haramta tafiye-tafiye har zai baba-ta-gani

A ranar Talata ne hukumomin Najeriya suka sanar da samun mace ta farko da ta kamu da cutar numfashi ta coronavirus a Najeriya, tun bayan bullarta kasar ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

Gwamnatin kasar ta ce ta dauki wasu matakai na hana bazuwar cutar a kasar.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakan ne bayan zaman farko da kwamitin yaki da cutar wacce aka sauya mata suna zuwa  COVID-19 da kasar ta kafa, a wani matakin riga-kafi da nufin dakile bazuwar cutar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana ta a matsayin annoba ta duniya.

Sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ne ya sanar da matakan jim kadan bayan kammala zaman kwamitin, inda yace matakin farko da kwamitin ya yanke shawarar dauka shine haramta wa jami’ai da ma’aikatan gwamnati tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje.

“An kuma soke duk wasu tafiye-tafiye da aka tsara yin su a baya,” in ji sakataren gwamnatin.

Haramta tafiya-tafiyen  zai ci gaba da aiki har sai baba-ta-gani,” kamar yadda sakataren gwamnatin ya fada.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More