DA DUMI DUMI: Abba kyari ya rasu

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya, Malam Abba Kyari ya rasu a jahar Legas, bayan da ya kamu da Coronavirus kuma aka kai shi jahar dan cigaban da karbar kulawa.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari Femi Desina ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a 17 ga watan Aprilu 2020 da misalin karfe 12.50 na tsakar dare a shafinsa Twitter.

A ranar 25 g watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyar ya kamu da Coronavirus bayan komawarsa Najeriya daga kasar Jamus.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More