DA DUMI- DUMI: An saki Orji daga gidan yari

Tsohon gwamnan jahar Abia, sanata Orji Uzor Kalu mai ci da kotu ta yanke wa  hukuncin zaman kidan kaso na shekaru 12 bisa  laifin almundahanan kudin jaharsa ya shaki iskar yanci, wanda hakkan ke nufin an sake shi daga gidan kaso.

Sanata Orji Kalu  ya samu fitowa daga gidan kaso na  Kuje dake  Abuja a safiyar yau Juma’a 8 ga watan Mayu 2020.

 Premium Times rawaito cewa an garzaya da shi gidansa dake cikin fadar shugaban kasa kan titin Queen Amina.

Sai dai wayanda suka tabbatar wa da manema labaren hakkan,  sun bukaci a sakaye sunayensu, bisa dalilin su na rashen bukatar  izini daga Orji Kalu kafen su sanar da hakkan.

An saki Mista Kalu ne yan dakika kadan bayan kotun koli ta soke hukuncin daureshi na tsawon shekara 12 da aka yanke masa  a watan Disamba shekarar  2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More