DA DUMI-  DUMI: Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya soke rudunar SARS

Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaki da fashi da makami a Najeriya wato SARS a jahohi 36 na ka kasar.

Adamu Muhammad Ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabin kai tsaye ga manema labarai a yau Lahadi 10 ga watan Oktoba, a babban birnin  Abuja.

Matakin ya biyo baya ne bayan  jerin zanga-zangar da aka dauki kwanaki ana yi a wasu jahohin kasar, wanda har a kasar waje an gudanar da zanga-zangar a yau.

Ana  zargin rundunar da ke yaki da fashi da makami ta SARS  da kisa, tozartarwa, cin mutuncin da yawan al’ummar kasar ta Najeriya.

Babban sufeton yan sandan ya kai kara wajen shugaba Buhari, sannan yanke hukuncin hakan ka iya biyo baya ne bayan shugaban ya amince, ko ya bada izinin aiwatar da hakan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More