DA DUMI-DUMI :Buhari na shiga ganawar sirri tare da Jonathan

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya soma wata ganawar sirri tare da tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan a fadarsa ta Aso rock da ke Abuja.

A tunanin ku me zasu tattauna?

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan abin da shugabannin ke tattaunawa a kai.

Bayanai sun ce Mista Jonathan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 11 na safe kuma take ya wuce ofishin shugaba Buhari.

A makon da ya wuce ne Jonathan ya jagoranci tawagar wakilai na musamman na kungiyar Ecowas zuwa kasar Mali domin sasanta rikicin siyasa a kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More