DA DUMI-DUMI: Buhari ya aika takardar MTEF/FSP na 2020-2022 zuwa majalisar dattawan Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika takardar tsarin kashe kudi da dabarun kasafin kudi na 2020-2022 zuwa ga majalisar dattawa.

Hakan zai bayar da dammar gabatar da kasafin kudin 2020. Shugaban majalisar dattawa wato  Ahmed Lawan ne ya fitae da  sanarwar a yayin zaman na majalisa an yau Laraba 25 ga watan Satumba 2019.

Kudin da ake bukatar kashewa na kasafin kudin 2020 ya kasance naira tirliyan 9.97. Jami’an gwamnatin shugaba Buhari sun yi alkawarin gabatar wa da yan majalisa kasafin kudin 2020 da wuri.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More