DA DUMI-DUMI : #EndSARS :Tsohon dan takarar shugaban kasa  ya bukaci shugaban Tiwita ya biya tarar dala biliyan 1 ga gwamnatin Najeriya

Tsohon  dan takarar shugaban Najeriya  karkashin inuwa jam’iyyar APC,  Adamu Garba yayi karar shugaban Tiwita Jack Dorsey zuwa kotu.

Garba ya ce yayi karar Dorsey zuwa kotu  ne bisa dalilin goyon bayan masu zanga-zangar Endsars a Najeriya dayi.

Sannan kuma ya bukaci Jack Dorsey da ya biya tarar dala biliyan daya wanda yayi daidai  da Naira biliyan 380 ga gwamnatin Najeriya bisa shiga da goyon bayan da yayi na zanga-zangar ta EndSARS  wanda hakkan ya janyo  tashin hankula, asarar dokiyoyi da rayukan al’umma da tarzomar zanga-zangar ta haifar.

#oaktvhausa #oaktvonline #EndSARS

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More