DA DUMI-DUMI: Fadar shugaban kasa ta dakatar shugaban EFCC Magu

Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta Najeriya EFCC.

Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

 A ranar ta Litinin ne rahotanni suka nuna cewa jami’an tsaron DSS a kasar sun kama Ibrahim Magu, har ta kai ga ya kwana  hannun jami’an ‘yan sanda masu gudanar da bincike

Sai dai wata sanarwa da DSS da kuma EFCC suka fitar daban-daban sun ce ba kama Mr Magu ta yi ba.

EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami’an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More