DA DUMI- DUMI: Farashin shinkafa babban buhu zai koma 16000 a Kano

Gwamnatin jahar Kano ta cimma matsaya da kungiyar masana’antu masu samar da shinkafa ‘yar gida,kan farashin babban buhu a kan Naira 16000 a zaman da su ka gudanar na yau Asabar 9 ga watan Mayu 2020.

Shugaban hukumar karfar korafe-korafe da yakar cin hanci da rashawa ta jahar,Barasta Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, zaman tattaunawar ba shi da nufin sanya matsin lamba ga masu samar da shinkafar,sai don samar da tsaftataccen yanayin kasuwanci a tsakanin masu saye da sayarwar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More