DA DUMI DUMI: Ganduje ya sassauta doka don yin cefanin azumi

Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita ta da sanya a makon da ya gabata don gudun yaduwar cutar.

Mataimakin gwamnan jahar Kano,kuma shugaban kwamitim karta-kwana na yaki da Coronavirus a Kano dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ne ya sanar da hakan yayin  da yake ganawa da manema labari a gidan gwamnatin Kano  An sassauta dokar ne daga karfe 6:00 na safiyar ranar Alhamis  zuwa karfe 12:00 na dare domin bawa al’ummar  damar yin cefanin azumin watan
Ramadana.
Amadadin gwamnan jahar Kano,  Gawuna ya ce sassauta dokar ya zama dole domin bawa al’ummar jahar damar  shirin azumin watan Ramadana kamar yadda aka saba yi a  kowacce shekara.
A karshe ya roki al’ummar jahar Kano da su cigaba da bawa  gwamnati hadin kai a kokarinta na dakile yaduwar annobar ta  covid-19 a jahar, bisa matakin da ta dauka, idan akayi lakari da yadda Coronavirus ke yaduwa a jahar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More