DA DUMI: DUMI – Gwamna Okowa na jahar Delta tare da matarsa sun kamu da Coronavirus

Gwamma jahar Delta Ifeanyi Okowa, Okowa, tare da matarsa, Edith sun kamu da cutar Coronavirus.

Gwamna Okowa ya fitar da sanarwar hakkan ne a shafin sa na Twitter a yau Laraba 1 ga watan Yuli 2020.

“Ni da matata, sakamakon gwajin mu ya nuna cewa muna dauke da kwayar cutar Covid19,mu na kula da lafiyar mu tare da cigaba da killace kanmu”. Inji Gwanman.

sannan ya kara da cewa,  Muna mika godiya ga dukkanin wayanda suke cigaba da taya mu da addu’a, damu da diyar mu.

Okowa shi gwamna na shida a kasar Najeriya wanda suka kamu da cutar da Coronavirus.

Gwamnan Okowo sun killace kansu tun a satin da ya gabata, bayan da daya da cikin yaransa ta kamu da cutar ta Coronavirus.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More