DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Najeriya  ta janye dokar  haramta jirgin Emirates daga kasar

Gwamnatin  Najeriya ta janye dokar haramta wa jirgin Emirates daga shiga kasar Najeriya.

“Hadaddiyar Daular Larabawa UEA ta rubuto wa kasar cewa, sun yarda su  baiwa yan Najeriya Visa, wanda hakan ne yasa Najeriya ta yanke  shawarar,  ta yarda jirgin na Emirates ya shigo kasar ta Najeriya”. Kamar  yadda Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya ya wallafa  shafinsa na tuwita a yau 30 ga watan Oktoba 2020

Minista Sirika yace , za fara bada Visar bisa tsarin doka, sannan kuma ya bada hakurin  bisa sabon yanayi da aka shiga tare da yin godiya ma tarin yawa.

Gwamnatin Najeriya ta  haramta wa jirgin Emirates shiga Lagos da Abuja ne  a ranar Juma’a 18 ga watan Satamba 2020.

Wanda hakan ya dau kwaniki 12 kafin gwamnatin ta janye dokar.

#OakTVHausa #OakTV
#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More