DA DUMI- DUMI : Gwamnatin tarayya ta dakatar da jami’an EFCC guda 12

Rahotunni daga jaridun kasar na nuna cewa, gwamnatin Najeriya ta dakatar da manyan jami’an hukumar dake yaki da masu yiwa  tattalin arzikin kasar zagon kasa wato EFCC,  a yayin da bincike ke cigaba da gudana a kan Ibrahim Magu.

Legit ta rawaito cewa, majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana wa PM News a daren Talata cewa babban sakataren hukumar, Olanipekun Olukoyede , na cikin wadanda aka dakatar.

“An dakatar da jam’ian hukumar  ne don bada damar gudanar da bincike ba tare da wani tangarda ba, da kuma  zargin bisa laifuka daban-daban wanda ya hada da  almundahana, sannan  an kulle ofishohinsu don kau da dukkan wani yunkurin  sace wasu takardu a hukumar.” a cewar majiyar.

Olanipekun Olukoyede ya zama Sakataren hukumar EFCC ne watan Nuwamba shekarar 2018.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More