DA DUMI DUMI: Gwamnonin APC sun shiga taron gaggawa a Abuja

Gwamnonin jam’iyyar mai mulki wato APC sun shiga ganawa tare da Shugaban jam’iyyar na kasa,Kwamrad Adams Oshiomhole a babbar birnin tarayya Abuja.
 
Duba da cewa babu wata masaniya akan dalilin ganawar tasu zuwa yanzu.
 
ganawar nasu ba zuwa yanzu, amma ana sanya ran Oshiomhole zai sanar da gwamnonin bayanai akan wasu lamura ciki harda rikicin da ake fama dashi a cikin jam’iyyar.
 
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi yace yana da yakinin samun tikitin APC a zaben na fidda gwani.
 
Gwamnan ya bayyana hakan ne a babban birnin jahar Kogi wato Lokoja,jim kadan bayan da ya fito daga dakin da jam’iyyarsa ta APC ke tantance ‘yan takarar gwamna.
 
A cewar gwamna Bello shi ne zai lashe zaben fidda gwani na APC wanda aka saka ranar yinsa a ranar 29 ga watan Agusta 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More