DA DUMI-DUMI: INEC ta bawa Yahaya Bello takardar shaidar lashe zaben Kogi

Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya karbi takardar shaidar lashe zaben daga hannu INEC a yau 21 ga watan Nuwamba 2019, bayan kwana 3 da gudanar da zaben a jahar ta Kogi.

Jami’in zaben, kuma mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zari’a wato ferfesa Ibrahim Umar ne ya damka masa takardar shaidar tare da mataimakin sa Edward Onoja.

Taron ya samu hallarta kwamishina yansandan jahar ta Kogi Wilson Inalegwu, manyan jami’an gwamnati tare shuwagabanin jam’iyyar APC.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More