DA DUMI-DUMI: INEC ta saka ranar zaben cike gurbi a Kogi

 

Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasar Najeriya wato INEC ta sanya ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben ciki gurbi na yan takarkarun majalisar dattawa ta kasa, wato Dino Melaye na karkashin jam’iyyar PDP da kuma Smart Adeyemi na karkashin jam’iyyar APC.

Kamar yanda kuka sani, kwana uku da suka wuce ne aka gudanar da zaben sanata a jahar Kogi a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019, wanda hukumar zaben ta ce zaben Sanata da aka gudanar a Kogi bai kammalu ba, kasancewar kuri’un da aka soke sunfi yawan wadanda ke kan gaba ya bada tazara.
Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ke kan gaba da kuri’u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam’iyyar PDP ke da kuri’u 59,548.
Amma sai dai, tun kafin bayyana sakamakon zaben ne Dino Melaye yayi watsi da sakamakon da ake tattarawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More