DA DUMI-DUMI: INEC ta soke wasu jam’iyun zabe

Duba ka/ki ga wannene

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Najeriya wato INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74 a Najeriya.

Sakamakon hakan yasa yanzu Jam’iyyun guda yanzu 16 ne suka rage.

Legit ta rawaito cewa, shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa aka soke jam’iyyun.

Dalilan sune:

1. Saba dokokin rijistan jam’iyyar siyasa a Najeriya

2. Gaza samun 25% na kuri’u a jaha ko daya a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kawanakin baya, sannan gaza samun 25% na kuri’u a karamar hukuma ko daya a zaben gwamnonin jahohi 36

3. Gaza samun nasarar lashe zabe a yanki daya, a zaben shugaban karamar hukuma na kananan hukumomi 774, gaza samun nasarar lashe zabe kujerar dan majalisa daya a jahohin Najeriya tare da gaza samun nasarar lashe zabe kujeran kansila ko daya.

Jam’iyyun da suka rage yanzu a fadin tarayyar ta Najeriya sune:

• Jam’iyyar AA
• Jam’iyyar AAC
• Jam’iyyar ADC
• Jam’iyyar APC
• Jam’iyyar ADP
• Jam’iyyar APGA
• Jam’iyyar APM
• Jam’iyyar LP
• Jam’iyyar NNPP
• Jam’iyyar NRM
• Jam’iyyar PDP
• Jam’iyyar PRP
• Jam’iyyar SDP
• Jam’iyyar YPP
• Jam’iyyar ZLP
• Jam’iyyar BP

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More