DA DUMI-DUMI: Kotu ta bada belin Maina kan naira biliyan 1

Babban kotun tarayya dake babban birnin  Abuja ta baiwa tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fanshon Najeriya garanbawul AbdulRashid Maina, belin naira biliyan daya tare da mutane biyu da zasu tsaya masa da kwatankacin  kudin belin.

Alkalin kotun Jastis Abang, ta bayyana cewa wajibi ne mutanen da zasu tsaya masa su kasance Sanatoci, kuma suna gidaje a unguwar Maitama ko Asokoro a Abuja,fasfo na Najeriya, fasfo na diflomasiyya, fasfo na musamman (ma’aikacin hukuma ko gwamnati) idan da akwai  da takardar shaidar biyan haraji na shekara uku. Sannan alakalin ya bayyana cewa a duk lokacin da da kotun ta neman wayanda suka tsaya masa zasu bayyana a kotun, tare  da yin rantsuwa akan zasu iya biyan kudin belin na Maina.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More