DA DUMI-DUMI: Kotu ta soke zaben Alhassan Doguwa

Kotun daukaka kara da ke zama a jahar Kaduna ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa, wato Alhassan Ado Doguwa a yau Litinin 4 ga watan Nuwamba 2019. Ta kuma bukaci sake zaben a wasu yankin.

Alhassan Ado Doguwa shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya.

Kotun ta  soke zaben na kananan hukumomi biyuwajen bayyana zaben a matsayin mara inganci. Mai shari’a Justice Oludotun Adefope-Okojie ya ce, bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zabe ba zai yiwu ba, domin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta cire sunayen wadansu jam’iyyun a yayin bayyana sakamakon zaben.

Kotun ta ce INEC ta karya doka ta hanyar rubuta sakamakon zaben jam’iyya biyu kawai cikin 53 da suka shiga zaben a takardar  mai lamba 0EC 8 (II) E. A don haka kotu ta nemi INEC ta sake shirya wani zaben nan da kwana 90 a yankin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More