DA DUMI – DUMI Kotun Koli Ta Rushe ‘Yan Takarar APC A Zamfara Ta Ba PDP Kujerar Gwamna

Babbar kotun kolin Najeriya ta ce jam’iyyar APC ba ta yi zabukan fitar da gwani ba, don haka jam’iyyar da take bin APC a yawan kuri’u ita ce ta lashe zabukan jahar da aka yi a watan Maris 2019.

A zaman kotun na yau Juma’a 24 ga watan Mayu 2019 kotun kolin ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba gabanin babban zaben da aka gabatar na shekarar 2019 a jahar.

Hukuncin kotun ya jaddada hukuncin da kotun daukaka kara a jahar Sakkwato ta yanke, wadda ita ma ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jahar.
Kotun kolin ta ce jam’iyyar ba ta da halatattun ‘yan takara don haka ba za ta iya kasancewa ta lashe zabukan da aka gudanar a jahar ba.

A kashe kotu tayi umarni da abawa wayanda suka yi  kara naira miliyan 10, sai dai daukaka kara bayi yi umarnin a bada kudi ba, amma ta amince da hukuncin kotu kolin ta zatar.

Sanata Kabiru Marafa ne ya fara shigar da kara a gaban kotu, inda ya kalubalanci zaben fidda gwanin da APC ta yi.
Jam’iyyar adawa ta PDP a shafinta na Twittwr ta wallafa hoton wanda ya yi mata takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar, inda ta ce dimokradiyya ta yi nasara,hakkan kazalika wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar PDP na bayyana farin cikin su tara da taya Bello Matawalle murna a shafikan su na sada zumuta, nacewa ya zana gwamnan jahar Zamfara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More