DA DUMI DUMI: Kotun ta soke nasarar Dino Melaye a matsayin sanatan Kogi

Kotun sauraron korafin zaben majalisar dokokin tarayya da ta jahar  Kogi ta soke nasarar zaben Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawa Najeriya.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Dino a matsayin wanda ya lashe zaben sanata da aka gudanar a watan Fabrairu 2019, sai dai Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ya tunkari kotun zaben domin kalubalantar zaben, wanda ke nuna cewa yana da ja lamarin.

Smart ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a zaben da suka hada da magudi, yawan kuri’u da suka wuce ka’ida da kuma rashin bin dokar zabe.

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Justis A. O. Chijioke a wani hukunci da suka zartar a ranar Juma’a  23 ga watan Agusta sun amince da hujojjin da Smart ya kafa inda suka yi umurnin sa zabe a yankin.

Sanata Melaye ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
 
Sannan ya kara da cewa wannan hukunci ba zai sa shi ya raba hankalinsa ba dangane da aniyyarsa ta neman zama gwamna a jahar Kogi ba, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More