DA DUMI-DUMI :Kwamishinan da Ganduje ya sauke ya kamu da Coronavirus

Tsohon kwamishinan ayyukan  na jahar Kano, Mu’azu Magaji wanda  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke sakamakon ‘yin murna’ da mutuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, ya fitar da sanarwar cewa ya kamu da cutar Coronavirus .

Ya wallafa hakkan  ne  a wani sako da a shafinsa na Facebook a yau  Alhamis 7 ga watan Mayu 2020.

Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce yanzu haka yana cibiyar killace masu dauke da Coronavirus a jahar Kano.

Ga sakon da ya wallafa a shafin nasa: Da safiyar nan sakamakon gwajin da hukumar dakile yaduwar da cututtuka ta Najeriya  wata NCDC ta yi min ya fito.
Kuma an tabbatar ina dauke da cutar Covid-19, kuma an kai ni cibiyar kula da masu dauke da cutar. A taya ni da addu’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More